Shugaba Nkurunziza ya bukaci tabbatar da tsaro a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Pierre Nkurunziza

A jawabin da ya yi ga al'ummar kasarsa, Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya jaddada bukatar da ke akwai ta hada kai domin samar da cikakken tsaro a kasar.

Wannan jawabi dai ya zo ne mako guda bayan rantsar dashi a matsayin shugaban kasar karo na uku wanda ya samu suka daga abokan adawa.

Wannan mataki na tazarcen shugaba Nkurunziza ya janyo zanga-zanga da kuma kokarin juyin mulki a kasar.

Shugaban kasar ya ja hankalin kwamitin da ke tabbatar da tsaro a cikin kasar da ya tabbatar ana aikin gudanar da tsaron rayukan 'yan kasar ba dare ba rana domin tarwatsa wadanda ya kira masu kokarin kashe mutane ba bu laifin tsaye ballantana na zaune.

Shugaban kasar ta Burundi ya kuma ce za a fara bawa matasa musamman daliban jami'oi horo na musamman.