Dangote zai gina kamfanoni a kasashe takwas

Image caption Dangote shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika

Kamfanin siminti na Dangote a Nigeria ya sanya hannu a kwangilar sama da dala biliyan hudu da miliyan dari uku, tare da wani kamfanin kasar China mai suna Sinoma International Engineering domin gina kamfanonin siminti a wasu kasashen Afrika.

Kamfanin siminti na Dangote zai gina kamfanonin simintin ne a kasashen Kamaru, Habasha, Kenya, Mali, Nepal, Niger, Senegal da kuma Zambia.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne ya sanya hannu a madadin kamfaninsa a wani biki da aka gudanar da Lagos, cibiyar kasuwancin Nigeria.

Idan aka kamalla gina wadanda kamfanonin simintin, kamfanin Dangote zai dinga samar da tan miliyan 50 na siminti daga tan miliyan 25 da yake samarwa a yanzu.