Yaki da shan barasa a Kenya

Image caption Mutanen da ke samun kulawa a cinbiyar yaki da barasa sua shan shayi.

Kasar Kenya ta bayar da sanarwa a kan tsauraran matakan da ta dauka a kan shan barasa, inda wani wakilin BBC ya bayar da rahoton cewa, mutane da dama na samun kulawa har ma an mayar da filin kallon kwallo a matsayin cibiyar kula da masu matsalar shaye-shayen barasa.

An ji ta bakin wasu mutane, amma an canza sunayen su.

Image caption Anne Wanjiku ta kashe makuden kudade wajen sayan barasa har sai da ta kasa biyan kudin makarantar yaranta.

Anne Wanejiku wacce kowa a filin kwallon ke kira 'cucu' watau ma'ana 'Kaka' da yaren 'yan kabilar Kikuyu, tana da shekaru 56 kuma tana daya daga cikin mata biyar da ake kula da su saboda shaye-shayen barasa.

Tsauraran matakai na kwana-kwanan nan da Kenya ta dauka ga masu shan barasa ba bisa ka'ida ba da kuma masu sha da basu kai shekaru a doka ba, da kuma sabuwar cibiyar kula da masu matsalar shaye-shaye, na cikin sababbin tsarin dokokin kasar da aka fitar.

"Da idanu na na ga wadanda suka makance kuma suka rasa rayukan su sakamakon shan barasa," In ji Wanjiku.

Ta nuna idon ta daya cikin raha, tana mai cewa, "Na yi sa'a ni ido daya na rasa".

Duk da haka ta ci gaba da shan barasa.

'Abinci sau uku'

A cikin makonni uku da bude cibiyar ta kula da masu matsalar shaye-shayen barasa, an samu kafa tantuna a filin kwallon, inda mutanen da ke bukatar taimakon sun karu zuwa sama da 700.

Duk wanda ya zo zai samu makwanci a cikin tantin, da abinci sau uku a rana da kuma kula da shawarwari, amma dole su zauna har watanni uku.

Image caption An bar wani fili domin shakatawa.

Hukumomin kasar suna kyautata zaton za a samu karin mutanen da za su kai har 5,000 kuma hakan ya sa suka fara kafa karin tantuna, amma akwai wani fili da aka kebe domin shakatawa, inda ake buga kwallo kuma a sha iska.

Wakilin BBC ya ce ya tarar da 'yan sanda da lauyoyi har ma da wani likita, duk suna samun kulawa.

Wani mutum ya ce yana kewar gida, amma shi ba zai tafi ba sai ya kammala wa'adin zaman neman kulawar.

Image caption Masu zuwa neman taimako dole su zauna har watanni uku.

Mr. Wa Iria, gwamnan garin ya shaida wa BBC cewa matasan suna samun goyon baya daga kungiyar matasa da suka kafa, inda suke taimakawa juna, suna kuma samun horo a kan aikin hannu da kananan sana'o'i.