'Yan ci rani 40 ne suka mutu a taken Libya.

'Yan Ci - rani Hakkin mallakar hoto AZZARO AFP
Image caption 'Yan Ci - rani

An gano gawar 'yan ci rani akalla 40 a cikin wani jirgin ruwan da ya samu tangarda a gabar tekun Libya.

Kafofin watsa labarai a Italiya na bayar da rahoton cewar watakila wadanda abun suka shafa sun mutu ne sakamakon sukewa.

A makon da ya wuce mutane 50 suka mutu a irin wannan yanayi.

Wasu yan ci ranin fiye da 400 ne jirgin ruwan kasar Sweden ya ceta daga cikin jirgin ruwan a yau.

Mai magana da yawun kamfanin dillancin labarai na Reuters ta ce mutane kusan 430 aka kubutar.

A baya-bayan nan dubannin wasu yan ciranin ne suka mutu yayin da aka kubutar da karin wasu dubannin bayan da aka bi sawun wani jirgin ruwan da ya fito daga kasar Libya.

Har yanzu dai babu tabbaci kan yadda yan ciranin da aka gano suka hallaka.

Amma an fi kyautata zaton sun mutun ne sakamakon sukewa, inda daga bisani wadanda suka tsiran suka bayyana cewa masu fasa kwaurin na su ne suka tilasta musu cigaba da zama a wuri guda.