An kama makudan kudaden jabu a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaron Nijar na yaki da masu almundahana.

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun ce sun kai samame wani waje, inda suka kwace makudan kudaden jabu na kasashen waje.

Gidan talabijin gwamnatin kasar ya ambato jami'an tsaron suna cewa sun kwace a kalla CFA 270m da euro da kuma daloli na jabu a garin Takieta na yankin Zinder .

Kazalika, jami'an sun ce sun kwato fasfo-fasfo da takardun motoci da lasisi na jabu.

Sai dai jami'an sun ce mutanen da ake zargin da hannu a wajen ajiye kayayyakin jabun sun tsere, suna masu cewa sun samu makamai uku a wajen.

Dokar kasar dai ta tanaji daurin shekaru goma a gidan yari a kan duk wanda aka samu da laifin ta'ammali da takardun jabu.