An zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu mutanen ne da laifin kisan kai da safarar kwayoyi.

Hukumomi a kasar Saudiyya sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane hudu ranar Laraba.

Uku daga cikin mutanen 'yan kasar ne da aka samu da laifin kisan kai; na hudu kuma dan kasar Syria ne da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu, an yanke hukuncin kisa a kan mutane 130, lamarin da ke nuna karuwar wadanda ake yankewa hukuncin kisan.

A ranar Talata, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta soki kasar ta Saudiyya a kan abin da ta kira "hanyoyin yanke hukuncinta masu cike da kura kurai", kana ta bukaci a dakatar da yanke hukuncin kisa.

Yawanci ana fille kan mutanen da aka samu da laifin kisan kai da fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da kuma ridda ne a bainar jama'a.