An kashe 'yan jarida biyu a Amurka

Image caption 'Yan jaridar sun gamu da ajalinsu a lokacin suna bakin aiki

An harbe har lahira wasu 'yan jarida biyu a jihar Virginia a Amurka lokacin da suke daukar wata hira ta talabijin.

Wani hoton bidiyo da aka sa a shafin YouTube ya nuna wata 'yar jarida ta fara hira da wani bako, kafin a ji karrar harbin bindiga har sau takwas, sai kyamarar ta fadi kasa kuma ana iya jin ihu.

Gidan talabijin din da 'yan jaridar kewa aiki, WDBJ7, ya ce wadda ke hirar Alison Parker da mai daukar mata hoto, Adam Ward dukkansu sun mutu a lamarin da ya faru a rukunin shaguna na Bridgewater da ke garin Moneta a karamar hukumar Bedford.

'Yan sanda sun ce ba a ga wanda ya kai harin ba kawo yanzu.