Ana zaman dar-dar a Misau

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An tura jami'an tsaro domin kwantar da hankali

Ana zaman dar-dar a masarautar Misau ta jihar Bauchi sakamakon bore daga wasu matasa kan nadin sabon sarki.

Rahotanni sun ce an kona wani bangaren na gidan Sarkin Misau da wasu motoci sakamakon nada sabon sarki, Alhaji Ahmed Sulaiman wanda gwamnatin jihar Bauchi ta yi.

Matakin bai yi wa wasu 'yan masarautar dadi ba abin da ya sa suka bazama kan tituna suna ta lalata dukiyoyin jama'a.

A halin da ake ciki dai an baza jami'an tsaro a garin, wadanda suka yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen kwantar da tarzomar.

A ranar 17 ga wannan watan ne Allah Ya yi wa Sarkin Misau, Alhaji Muhammadu Manga na uku rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Masarautar Misau tana daya daga cikin masarautu masu rike da sarauta mai daraja ta farko a jihar Bauchi.