Saudiyya: Ana samun karuwar cutar MERS

Hakkin mallakar hoto Getty

Wasu alkaluma daga Ma'aikatar lafiyar kasar sun nuna cewa mutum 17 ne suka rasu a cikin makon da ya wuce.

Kuma a makon jiyan ma sai da aka rufe sashen kula da majinyata na gaggawa, bayan wani jami'i a sashen ya harbu da cutar, a Riyadh, babban birnin kasar.

Wannan annobar dai na yaduwa ne a daidai lokacin da kimanin musulmi miliyon biyu ke shiga kasar don yin aikin hajjin bana.

Dr Ha'il al-Abdeli kwararre a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa a ma'aikatar lafiya ta Saudiyya yace suna daukar matakai domin hana yaduwar cutar.