Ana son halasta karuwanci a Uganda

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An samu karuwar masu kamuwa da HIV da kashi 7.3 a tsakanin 'yan kasar masu shekaru 15 zuwa 49.

Kungiyoyin kare hakkin bil adam sun bukaci a halasta yin karuwanci a kasar Uganda.

Wata karuwa, Diana Natukunda, ta shaida wa wakilin BBC a Kampala cewa tana son yin karuwanci ba tare da fuskantar matsi daga wajen hukuma ba, tana mai cewa tana "son a ba ni kariya kamar yadda ake bai wa kowanne dan Uganda".

A cewar Natukunda, hakan zai rage yaduwar cutar HIV domin kuwa karuwai za su rika amfani da matakan kariya gabanin yin jima'i.

Sai dai ra'ayoyin 'yan kasar sun sha bamban game da batun.

Wasu 'yan kasar na ganin bai kamata a halasta karuwanci ba, yayin da wasu ke ganin ya kamata a bai wa kowa 'yanci ya yi abin da yake so.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu karuwar masu kamuwa da HIV da kashi 7.3 a tsakanin 'yan kasar masu shekaru 15 zuwa 49.