Boko Haram ta kashe soja da fararen hula a Niger

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption 'Yan Boko Haram sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a Jamhuriyar Nijar.

Wasu mutane da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kudancin Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani soja da fafaren hula guda biyu.

Jami'an tsaron kasar sun ce an kai harin a yankin Diffa kusa da garin Abadam da ke kan iyakar kasar da Najeriya.

Sun kara da cewa maharan sun sace kayayyaki a shagudna bayan kashe mutanen.

Kimanin mutane150,000 suka tsere daga Najeriya zuwa yankin na Diffa a cikin shekaru biyu da suka.