Boko Haram: Chadi ta yanke hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Chadi ta yanke hukuncin kisa a kan 'yan Boko Haram su goma.

Wata kotu a Chadi ta yanke hukuncin kisa a kan wasu 'yan kungiyar Boko Haram su goma sakamakon samunsu da ta yi da laifin ta'addanci, bayan an shafe kwanaki uku ana musu shari'a a N'djamena babban birnin kasar.

An yanke masu hukuncin ne saboda samunsu da hannu a hare-haren da aka kai a birnin na N'djamena a tsakanin watannin Yuni da Yuli, inda mutane 53 suka rasa rayukansu.

Wadannan ne hare-hare na farko da kungiyar Boko Haram ta kai kasar Chadi, inda aka kafa hedikwatar rundunar sojin hadin gwiwa ta kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi domin yaki da ta'addanci.

A watan Yuli ne kasar Chadi ta sake dawo da hukuncin kisa a kan duk wanda ya aikita laifin ta'addanci a kasar.