Mutane 1bn na shiga Facebook kullum

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane biliyan daya a duniya suna shiga shafin facebook a rana.

Mark Zuckerberg, wanda ya kirkiro Facebook ya jinjina wa kamfanin sa saboda ci gaban da ya samu na mutane biliyan daya sun shiga shafin a rana daya.

Ya bayyana cewa wannan wani sabon cigaba ne, kuma mafarin hada zumunci ne a duniya baki daya.

A wani jawabi da ya wallafa a shafin sa na Facebook din, Mr. Zuckerberg ya ce wannan adadi na nuna cewa, mutum daya cikin mutane bakwai a duniya suna amfani da shafin domin sada zumunta da 'yan uwa da abokan arziki.

A watan Oktoba na shekarar 2012 ne kamfanin ya yi bikin samun mutane biliyan daya da suke mu'amala da shi.