Mutane 20 sun mutu a tsibirin Karebiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ambaliyar Ruwan Dominica

Firaministan Dominica da ke tsibirin Karebiya ya ce ya zuwa yanzu an gano mutane 20 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa wadda tsawa da iska mai karfi suka haddasa.

A cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talbijin din kasar, Roosevelt Skerrit ya ce daruruwan gidaje da gadoji da kuma tituna sun lalace.

Barnar da ambaliyar ta haddasa ta barnata cigaban da tsibirin ya samu shekaru 20 da suka gabata.

Yanzu haka guguwar da ke tare da ambaliyar na nan na ratsawa ta cikin Haiti da kuma Jamhuriyar Dominican, kuma karfin tafiyar ta ya kusa kaiwa kilomita 85 a cikin sa'a guda.

Sai dai masana sun ce karfin guguwar na raguwa.