SSS ta dakile shirin Boko Haram na leken asiri

'Yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Hukumar ta ce a sakamakon hadin guiwa tsakaninta da jami'an tsaro na filin saukar jiragen samar na Nnamdi Azikwe, ta kama wani yaro dan shekaru goma sha hudu mai suna Sulaymon Abdulrahman wanda ake yiwa lakani da Sunday Ajayi, dan jihar Kogi.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, Abdulrahman ya ce wani ne mai suna Dauda Sadiq, ya umarce shi da ya nemi bayan sirri dangane da yadda al'amurra suke gudana a filin saukar jiragen samar, kamar tafiyen fasinjoji da yadda ake bincika su da kuma yadda suke shiga jirgin saman.

Hukumar ta ce a sanadiyyar haka ta na aiki da hukumomin kula da zirga zirgar jiragen sama domin hana afkuwa wani hari da kuma tabbatar da tsaro a filayen saukar jiragen samar.