Za a sanyawa Sudan ta Kudu takunkumin sayan makamai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Salva Kiir da Riek Machar

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gargadi bangarorin da ke yakar juna a Sudan ta Kudu akan cewa za su iya fuskantar takunkumin sayan makamai da kuma sauran takunkumi idan har ba su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ba.

Kwamitin ya fitar da wannan sanarwar ne bayan Shugaba Salva Kiir wanda ya amince tare da sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar laraba ya ce yana da shakku akai.

Jagoran 'yan adawa Riek Machar shima ya sanya hannu akan yarjejeniyar.

Akalla an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta har sau bakwai a baya inda ba a je ko ina ba kuma abin ya wargatse.