An gargadi 'yan Najeriya game da ambaliya

Image caption Wurin da ambaliyar ruwa ta shafa

Hukumomi a Nijeriya na ci gaba da kiraye-kiraye ga al'umomi dake zaune a yankunan da ake fargabar fuskantar ambaliyar ruwa, da su tashi daga yankunan.

Hukumomin sun bukaci mutanen su koma wasu wuraren domin kada ambaliyar ta rutsa da su.

Masana sun yi hasashen cewa a jihohi da dama na Nijeriya za a fuskanci matsalar ambaliyar ruwa bana, sanadiyar ruwan sama da kuma cika da batsewar koguna da tafkuna, inda tuni ma wasu yankunan suka fara fama da faruwar ambaliyar.

Alhaji Alhassan Barde, Sakataren Zartaraw na hukumar agajin gaggawa ta Filato, daya daga cikin jihohin da kusan a duk shekara ke fama da matsalar ta ambaliyar ruwa ya bukaci jama'a dake wuraren da ake fuskantar bala'in na ambaliya, su tashi zuwa tuddan kun tsira.

A bana, kawo yanzu, jihohi Katsina da Sakkwato da Yobe da Zamfara da Bauchi sun gamu da munanan bala'o'I na ambaliyar ruwa da suka yi sanadiyar hasarar rayukan mutane da gidaje da gonaki.