Bill Clinton ya yi jawabi a taron tunawa da Hurricane Katrina

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bill Clinton

Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya gabatar da jawabi a wani wurin taro da aka shirya domin tunawa da aukuwar bala'in Hurricane Katrina a birnin New Orleans shekaru 10 da suka wuce.

Mista Clinton ya nuna bukatar samun hadin kai domin taimakawa wajen magance matsalolin da birnin ke fuskanta har yanzu.

Tsohon shugaban kasar ya ce koda yake bai kamata ace za a kawar da kai daga nasarar da aka samu ba wajen sake gina birnin New Orlean, amma akwai sauran aiki a gaba ta yadda za a kawar da manyan matsalolin da suke kawo rashin daidaito a tsakanin jama'a, kamar banbancin launin fata da kuma karfin aljihu.

Wasu mazauna birnin na New Orleans sun musanta ikirarin da wasu ciki harda shugaba Obama suka yi cewa birnin ya zamo wani abin kwatance ta fuskan farfadowa.

Kimanin mutane dubu 1800 ne suka mutu a lokacin bala'in wanda kuma ya haddasa barna mai girma.

Tun da farko magajin garin birnin ya shaidawa dandazon mutanen da suka halarci taron tunawa da iftila'in cewa wasu mutane suna tunanin birnin ba zai taba dawowa hayyacin sa ba, amma kuma bayan shekaru 10, babu alamun tagayyara a tare da shi.