Ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a Malaysia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Najib Razak

Cuncurundon mutane ne suka mamaye titunan babban birnin kasar Malaysia Kuala Lumpur inda suke bukatar firaministan kasar Najib Razak ya yi murabus saboda wata badakalar kudi.

Masu zaga-zangar dai sun rinka ife-ife dan nuna adawa da gwamnatin kasar

Mafi yawancin su dai sun shafe daren farko a waje suna zanga-zangar.

'Yan sandan dai ba su dauki wani mataki akan masu zanga-zangar ba duk da hana wa da aka yi.

Mr Razak dai ya kori mataimakinsa daga aiki inda yake zargin sa da hannu a badakalar kudin wacce aka fara ta tun bayan da aka gano dala miliyan dari bakwai a asusun ajiyar sa na banki.

An sauya babban Lauyan gwamnatin kasar wanda ke bincike akan badakalar kudin.