Matsalar 'yan cirani ta shafi kowa

Laurent Fabius Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kullum yawan mutanen da ke yin tattaki dan ketarawa kasashen turai na karuwa.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya baiyana halayyar wasu kasashen turai dangane da matsalar da ake ciki ta 'yan cirani da cewa abin kunya ne.

Ya yi Allah wadai da wasu mambobin tarayyar turan musamman na gabashin turai bisa kin karbar yan gudun hijira.

Mr Fabius musamman ya yi kakkausar suka ga kasar Hungary saboda sanya shingen waya da ta yi akan iyakarta domin hana yan gudun hijirar da ke zuwa ta Serbia damar shiga kasar.

Ya ce wannan ko kadan ba martaba ba ce ta tarayyar turai. Faransar ta bi sahun kasashen Birtaniya da Jamus wajen kiran gudanar da taron gaggawa ta ministocin kungiyar tarayyar turai domin lalubo hanyar da za'a shawo kan lamarin karuwar kwararar yan cirani.