Gobara ta tashi a Saudiyya

Wani gini da ya kama da wuta a Saudi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rukunin gidajen mallakar wani kamfanin mai ne a kasar Saudiyya.

Hukumomi a Saudiyya sun ce wata gobara da ta tashi a wani rukinin gidajen ma'aikata na wani kamfanin mai na kasar ta hallaka mutane akalla mutane goma sha daya wasu fiye da dari biyu kuma sun sami raunuka.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su sun fito ne daga kasashe daban-daban, an baiyana cewa wasu daga cikin su suna cikin mummunan yanayi.

Gobarar ta tashi ne daga kasan hasumiyar ginin a gabashin birnin Khobar.

Kamfanin man Aramco yana da ma'aikata fiye da dubu hamsin yawancin su 'yan cirani.