An kama Kwamandojin Boko Haram a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Kungiyar Boko Haram

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram da kuma wasu 'yan kungiyar da dama a sassa daban-daban na kasar.

Hukumar ta ce ta yi kamen ne a ci gaba da matakan da take dauka na dakile hare-haren mayakan kungiyar.

Hukumar DSS ta ce matsin lambar da 'yan Boko Haram ke fuskanta a arewa maso gabashin kasar inda suke da karfi ne ya sa suka sauya salon kai hare-haren su a yanzu.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, hukumar ta DSS ta ce ta yi kamen ne a jihohin Legas da Kano da Filato da Enugu da kuma Gombe a cikin watan Agusta.

Hukumar ta bukaci jama'a da su rika taimakawa da bayanai game da take taken bata-gari.