'Yan bindiga sun sace 'yar jarida a Fatakwal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun ce suna yunkurin kubutar da 'yar jaridar.

Wasu 'yan bindiga sun sace wata fitacciyar 'yar jarida, Donu Kogbara, wadda ke yin aiki a kamfanin buga jaridun Vanguard.

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta ce an sace Kogbara ne ranar Lahadi a kusa da gidanta da ke babban birnin jihar, Fatakwal.

Kakakin rundunar, Ahmad Muhammad, ya ce suna nan suna kokarin kubutar da ita.

Har yanzu dai ba a san dalilin sace 'yar jaridar ba.

Birnin na Fatakwal da ma yankin kudu masu kudancin Najeriya ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.