Mutane 10 ne suka mutu a gobarar Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gobarar ta tashi ne a wani dogon gini na unguwar Radium a garin Khobar.

Mahukuntan Saudiyya sun ce 'yan kasar Canada uku da dan Najeriya da kuma dan Pakistan na daga cikin wadanda suka mutu a gobarar da ta lashe wata unguwa a kasar.

Gobarar ta tashi ne da safiyar ranar Lahadi a wani dogon gini na unguwar Radium a garin Khobar, inda nan ne akasarin ma'aikatan kamfanin mai na Aramco ke zama.

Mai magana da yawun hukumar tsaron gabashin kasar, Kanal Ali bin Saad al-Qahtani, ya ce mutane 10 ne suka mutu yayin da 259 suka samu raunuka.

Al-Qahtani bai fadi kasashen da sauran mutane biyar din da suka mutu suka fito ba.

Tun da fari dai hukumomin kasar sun ce mutane 11 ne suka mutu.

Wani bincike da aka gudanar ya yi zargin wata taransufomar wutar lantarki ce da ke can kasan ginin ta jawo gobarar.