Somalia na fama da karancin abinci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kashi daya cikin uku na jama'ar Somalia suna bukatar abinci

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tamowa da karancin abinci ya yi muni matuka a Somalia.

Majalisar ta ce yawan mutanen da ke fama da matsalar karancin abincin ya karu da kimanin kashi 20 cikin 100 a watanni shida da suka wuce.

Rahotanni sun ce lamarin na iya ta'azzara sakamakon karancin ruwan sama da kuma rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar.

Kusan kashi daya cikin uku na jama'ar Somaliya suna bukatar taimakon jin kai.

Mutane 250,00 suka rasu a kasar a lokacin wata matsananciyar annobar fari shekaru hudu da suka wuce.