An rantsar da Adesina a bankin AfDB

Hakkin mallakar hoto Afdb
Image caption Adesina ya sha alwashin bunkasa nahiyar Afrika

An rantsar da dan Nigeria, Dokta Akinwumi Adesina a matsayin sabon shugaban bankin raya kasashen Afrika watau AfDB.

Adesina ya maye gurbin dan kasar Rwanda, Donald Kaberuka wanda ya jagoranci bankin na tsawon shekaru 10 tun daga shekarar 2005.

A cikin watan Mayu aka zabi Adesina wanda shi ne tsohon ministan ayyukan gona a Nigeria.

Sabon shugaban ya ce a cikin shekaru biyar masu zuwa, bankin zai mayar da hankali ne a kan samar da lantarki a gidaje da kuma gina asibitoci da kuma makarantu.

Adesina ya ce dole ne a mayar da hankali wajen samar da ayyuka a tsakanin matasa a Afrika saboda a cewarsa, matasa su ne babban jarin Afrika.