An gurfanar da Sambo Dasuki gaban Kotu

Kanal Sambo Dasuki
Image caption Kanal Sambo Dasuki a kotu ranar Talata.

A ranar Talata ne hukumomin Nigeria suka gurfanar da tsohon mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro a gaban kotu.

Ana zargin Sambo Dasuki da mallakar makamai ba tare da lasisi ba, zargin da makusantan Sambo Dasukin suka ce ya musanta.

'Yan kwanaki bayan an sauke Sambo Dasuki daga mukaminsa na mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, jami'an tsaron kasar sun gudanar da bincike a gidajensa da ke Abuja da kuma gidan mahaifinsa da ke garin Sokoto.

A nan ne jami'an tsaron suka ce sun gano muggan makamai da kuma wasu motoci masu sulke da Dasukin ya mallaka ba bisa kaida ba.