Sabon tambarin Google

Hakkin mallakar hoto
Image caption Google ya ce tambarin da aka sauya nada sauki wajen fahimta da kuma launi mai ban sha’awa.

Kamfanin Google ya fitar da wani sabon tambari daya kunshin muhimman ayyukan sa.

Sauyin da aka yi a tambarin ya inganta fasalin haruffa da kuma launin da aka sani dauke da sunan kamfanin.

Kamfanin ya ce ana bukatan wannan sauyi saboda yadda mutane da dama yanzu ke amfani da wayoyin salula ta tafi da gidanka wajen shiga Google baya ga amfani da kwamfutar tebur da aka saba.

Wannan sauyin na zuwa ne bayan da Google ya sanya daukacin rassan sa karkashin kamfani guda da ake kira Alphabet.

Kamfanin ya ce tambarin da aka sauya nada sauki wajen fahimta da kuma launi mai ban sha’awa.