Hunagary ta kare matakinta kan yan ci rani

'Yan ci-rani a Hungary
Image caption 'Yan ci-rani a Hungary

Kasar Hungary ta kare matakin da ta dauka na rufe babbar tashar jiragen kasa dake Budapest babban birnin kasar ga 'yan gudun hijira dake ta kokarin zuwa kasashen Turai.

Daruruwan 'yan gudun hijira ne aka hana shiga jirgi zuwa Austria da Jamus.

Sai dai wani kakakin gwamnatin Hungary din Zoltan Kovacs, ya ce kasar na aiki ne da dokar tarayyar Turai. Inda ya ce kasar Girka ce kadai bata bin dokoki.

Ya ce,"ba a yadda da cewa Girka ta bar dubban 'yan gudun hijirar fita zuwa Hungary da ma wasu kasashen turai ba tare da an yi musu rijista ba."

A wani bangaran kuma, fada ya barke tsakanin 'yan gudun hijira da 'yan sandan Macedonia a kan iyakarsu da Girka.