An tarwatsa masu zanga-zanga a Beirut

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga sun shafe kwanaki suna fitowa kan tituna

'Yan sanda a Labanon sun dauki matakin tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke zaman dirshan a cikin ma'aikatar kula da muhalli da ke Beirut.

'Yan sandan sun tura masu zanga-zangar waje, bayan da suka yi wa ma'aikatar kawanya suka kuma tilastawa 'yan jarida fita daga wajan.

Masu zanga-zangar bangare ne na YOU STINK, kungiyar da ke fafutukar ganin an kashe shara, wadanda suka fusata akan rashin kwashe sharar da ta taru a birnin Beirut.

Sai dai yanzu kuma zanga-zangar ta fadada ya zuwa cin hanci da rashin iya aiki na 'yan siyasa.