Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan ci-rani na ci gaba da kwarara zuwa Turai

Austria ta karfafa binciken ababen hawa a yankunan kan iyakarta daga Gabashi, wadanda masu fatauci BilAdama ke amfani da su wajen tsallako da 'yan cirani cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Hakan ya janyo cunkoson motoci har na tsawon kilomita 20. A cikin watan Yuli dai, dimbin 'yan cirani ne suka cimma iyakokin Tarayyar Turai, fiye da a duk wani lokaci a baya.

To Birtaniya da Faransa da kuma Jamus, yanzu suna so a yiwa 'yan ciranin da ke isa Tarayyar Turai, rejista, tare da daukan hotunan zanen yatsunsu. Haka kuma sun kira wani taron gaggawa nan da makonni 2 masu zuwa.

Kudancin Turai ma na fama da wannan matsala inda daruruwan 'yan cirani ke isa tsibiran Girka a kowacce rana.

Ga rahoton Abdullahi Tanko Bala