An dade ana ci da gumin mu:matasan Niger Delta

Niger Delta Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'yan Niger Delta sun kwashe shekaru ana yanke musu alawus din su, amma yanzu hakan ta kau a cewarsu

Tsofaffin 'yan gwagwarmaya da makamai na yankin Naija Delta a najeriya sun kara dangane da yadda ake yake musu kudaden alawus din su.

Matasan wadanda gwamnatin Nigeria ta yiwa afuwa sun ce an maido da biyansu kudaden alawus na 65,000 a kowanne wata a yanzu kamar yadda aka tsara kuma aka fara tun zamanin gwamnatin marigayi Umar Musa 'Yar-Aduwa.

Matasan sun yi zargin cewa an kwashe shekaru ana biyansu naira 15,000 zuwa 20,000 wasunsu ma ba a ba su ko kwabo.

Amma da hawan gwamnatin Muhammdu Buhari zaluncin da ake yi musu ta kau domin ana biyan kowa hakkinsa yadda ya kamata kuma kamar yadda aka tsara a cewarsu.