Fada tsakanin 'yan gudun hijira da 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira sun cika wata tashar jirgin kasa a Budapest

Fada ya barke tsakanin 'yan sanda da 'yan gudun hijira a wajan babbar tashar jiragen kasa ta Budapest babban birnin kasar Hungary.

'Yan gudun hijirar na kara takaicin hana su shiga jiragen kasa zuwa Austria da mahukuntan ke yi.

Wani wakilin BBC da ke wajan ya ce 'yan sanda na ta kama matasan 'yan gudun hijirar a shagunan shiga intanet a kusa da wajan, kuma za su iya jefa su a jirgen da za su kai su sansanonin 'yan gudun hijira da ke gabashin kasar.

Wasu kasashen Turai kuma na daukar matakan gaggawa kan batun.

Girka ta yadda ta samar da karin wasu wuraran 'yan gudun hijirar yayin da ita kuma Italiya ta amince ta kara bincike a kan iyakar Austria, kamar yadda Jamus ta nema.