Za ayi fareti na musamman a China

Shugaban China, Xi Jinping zai jagoranci faratin da sojoji za su yi a Beijing domin tunawa da nasarar da China ta yi a kan Japan, a yakin duniya na biyu, shekaru 70 da suka wuce.

A ranar Alhamis ne za a gudanar da wannan faretin mai dimbim tarihi.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan fareti zai nuna alhini ga abinda 'yan kasar China ke cewa "Yakin da ya 'yanta China daga hannun Japan".

Alexander Neil daga Ma'aikatar Dabarun neman ilimi ta kasa da kasa, watau International Institute for Strategic Studies (IISS), zai gudanar da bincike a kan yadda alhinin zai kasance.

Fiye da mutane 10,000 ciki hadda dakarun sojin Peoples Liberation Army (PLA) da sojoji 1,000 masu mukami na musamman daga kasashe 17, za su yi jerin gwano har gaban butum-butumin Mao Zedong zuwa gaban Mambobin Poliburo na 'yan China, har ma gaban manyan shugabannin da za su zauna a dandalin Tiananmen.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masa jefa bama-bamai da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu zasu yi shawagi.

Kusan jirage 200 ne za su zagaye sararin samaniya a inda jama'a da suka hada da shugabannin kasashe 30 har ma da na Rasha Shugaba Vladmir Putin, wanda shi ma zai halarci taron.

'Gudunmuwar China'

Wannan farati zai bayar da damar fahimtar babban gudunmuwar da rundunar sojin China ta bayar domin samun galaba a yaki da Japan a shekarar 1945.

A lokacin da yakin ya barke a Turai a shekarar 1939, China ta riga ta shekara takwas tana cikin matsanancin hali sakamakon takurar da Japan ta yi masu bayan da ta mamaye kasar.

Hukumar watsa labarai ta kasar China ta bayyana cewar kusan sojojin Japan miliyan biyu ne, aka kashe a yakin duniya na biyu, kashi 70 cikin 100 cikin su kuma a kasar China suke.

Faratin da za'a yi ranar Alhamis din zai hada da rundunar sojin PLA da suke da tarihi a kan yaki da sojojin Japan, cikin su kuma har da rundunar hadin gwiwa ta 'Northeast United Anti-Japanese Force' da kuma dakarun China na 'South China Guerillas'.

'Yan gaba-gaba wurin kai hari'

Rundunar sojin China PLA ta bai wa sojoji mata damar taka rawa na musamman, inda mata 51 ne za su yi maci a matsayin sojoji masu mukami wadanda aka dauka aiki a farkon shekara.

Hakkin mallakar hoto chinafotopress
Image caption Sojoji mata zasu shiga faretin, inda har masu mukami na musamman ma zasu yi maci.

Tian Ou, wacce itac e mace Janar ta farko da ta shiga faratin, ita ce za ta jagorancin faratin.

Wani karin abun mamaki ga wannan farati kuma shi ne kasancewar abokan aikin Janar Tian su sama da 50, wadanda za su zama 'yan gaba-gaba a jagorancin faratin, kuma kafofin yada labarai sun bayar da rahotannin cewar duk sun zage damtse wurin rage kiba lokacin da ake horar da su.

'Zage damtse'

A baya a lokacin farati makamancin wannan, China ta fito da sababbin makaman yaki, da na'urorin daban-daban, amma ana zaton wannan karon abun zai kara inganta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masana suna kyautata zaton wannan fareti zai bayyana irin karfin da China ta tanada wurin yaki.

Rundunar sojin sama za ta fito da na'urar harba bama-bamai masu cin dogon zango da jiragen yaki da na'urar da ke bayar da alamun gargadi ga jirage masu saukar ungulu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption China ta so ta jaddada wa duniya matsayin ta da kuma goyon bayan da ta bayar wurin samun galiba a kan Japan.

Kasar China ta fuskanci rayuwa a matsanancin hali a baya, amma ta gano cewar gaba ta fi baya yawa, duk da ba za a manta ta baya ba.

Hakkin mallakar hoto european photopress agency
Image caption Shugaba Xi Jinping ya lashi takwabin kawar da duk wata husuma da China zata fuskanta.

Mutanen China ma sun san a wannan lokaci na faduwar tattalin arziki da kasar ke fuskanta, Shugaba Xi Jingping ya sha alwashin kare hakkokin kasar sa a duniya.