Dubban 'yan ci-rani sun isa Girka

Yan ci rani Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wasu daga cikin dubban 'yan ci rani da suka isa Girka

'Yan cirani sama da dubu hudu ne suka isa birnin Athens na kasar Girka daga tsibirin Lesbos.

Gwamnatin kasar ta ce ba ta da kudin da za ta dauki dawainiyar 'yan ciranin, sai dai kungiyoyin agaji sun ce ya kamata mahukuntan kasar su ba su kulawa.

A ranar Talata, shugaba Prokopis Pavlopoulos na kasar Girka ya kira takwaransa na kasar Faransa, Francoise Hollande ta wayar tarho inda ya nemi a gabatar wa kasashen Turai da halin da kasarsa take ciki na kwararar 'yan ci-rani.

A ranarLaraba ake sa ran Majalisar zartarwa ta Girkar za ta yi taro a kan batun.

A cewar jaridar Kathimerini 'yan ci-rani 17,500 aka yi wa rajista a makon jiya.

Kazalika wani jirgin ruwa da ke dauke da 'yan ci-rani 1, 749 ya isa garin Piraeus mai tashar ruwa da ke kusa da Athens a cikin daren ranar Talata.