An cire wa shugaban Guatemala rigar kariya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Perez Molina ya musanta zarge zargen cin hanci da rashawa da ake yi masa.

Yan Majalisun dokokin kasar Guatemala sun kada kuri'ar amince wa da cire wa shugaban kasar Otto Perez Molina rigar kariya daga fuskantar tuhumar sa bisa zargin cin hanci da rashawa.

Dinbim masu zanga zanga ne suka zagaye harabar Majalisar don bada kariya ga 'yan Majalisun dokokin yayin da suka fara hallara zauren Majalisar don kada kuri'ar.

Shugaba Perez Molina ya tsallake irin wannan kuri'a a watan daya gabata, sai dai masu gabatar da kara sun zarge shi da hannu dumu-dumu a badakalar cin hancin miliyoyin daloli a hukumar hana fasakwauri ta kasar, sai dai ya sha musanta zarge zargen da ake yi masa.

A ranar lahadi ne dai za'a gudanar da zaben shugaban kasar, kuma wannan kuri'ar da 'yan Majalisun suka kada matakin farko ne, yayin da shugaba Perez Molino ke dab da fuskantar shari'a kamar kowanne dan kasar Guatemala.