An soma shari'ar Ntaganda a kotun ICC

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Ana yi masa lakabi da Terminator, saboda shaharar da ya yi wajen kisan kai na ba-sani-ba-sabo.

Tsohon dan tawayen Congo, Bosco Ntaganda, ya ce ba shi da laifi bisa tuhumar da kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya, ICC, ke masa ta laifukan yaki.

Kotun, wacce ke birnin Hague, tana tuhumar Ntaganda ne da aikata laifukan yaki 18, cikin su har da kisan kai, yi wa yara fyade, da tursasawa mata yin lalata.

Kotun ta ce Ntaganda ya aikata wadannan laifuka ne a Gabashin Kongo, tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.

Mt Ntaganda, wanda ake sa ran zai ki amsa laifukansa, zai yi tozali da dumbin mutanen da suke zargin ya ci zarafin su.

A shekarar 2013 ya mika kan sa, yana mai bukatar a mika shi ga kotun ta ICC, bayan ya kwashe shekara da shekaru a fagen daga.

Ana yi masa lakabi da Terminator, saboda shaharar da ya yi wajen kisan kai na ba-sani-ba-sabo.