An kama 'yan jarida a Kamaru

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hukumomin kamaru na zargin 'yan jaridun da alaka da Boko Haram

Kungiyar kasa da kasa ta 'yan jaridu renon Faransa ta bukaci gwamnatin Kamaru da ta sako 'yan jaridu biyu da ta kame a arewacin kasar.

'Yan jaridun biyu Ahmed Abba na sashen Hausa na gidan rediyon RFI da kuma Simon Ateba na wata Cibiyar kasa da kasa an kama su ne a lokacin da suke gudanar da aikinsu a kasar.

Simon Ateba dai an kama shi ne a sansanin 'yan gudun hijira na Minawawo a yayin da yake binciken halin rayuwar 'yan gudun hijirar Najeriya a kasashen Chadi da kuma Kamaru. An kuma zarge shi da leken asiri.

Hukumomin kasar na zargin 'yan jaridun biyu da alaka da kungiyar Boko Haram sai dai har a yanzu ba a gurfanar da su a gaban kotu ba.