Sabuwar komfuta mai bangare-bangare

Image caption Sabuwar Komfuta mai kamar bulo ta kamfanin Acer

Kamfanin Acer ya kaddamar da sabuwar komfuta mai bangarori daban-daban wanda za'a rika harhada su kamar bulo.

Dalilin kirkiro wannan komfuta a cewar kamfanin Revo Build wadanda suka kirkiro ta shine don mai masu amfani su iya sarrafa ta yadda yake so ba tare da yin warware ta ba ta hanyar kwance noti-notin jikinta domin sa mata wani abu.

An dai sawwake yin hakan ne ta hanyar wasu maballai a sama da kuma kasar kowanne sashe mai kamar bulo wanda zai makale da dan uwansa.

Kamfanin na Korea ya baje wanna sabuwar komfutar ne a kasuwar baje kolin komfutoci wanda ake yi wa lakabi da Ifa a Berlin