Bubakar Keita yana ziyarar aiki a Nijar

 Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.  Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Ibrahim Boubacar Keita

Shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keita ya soma wata ziyarar aiki a jamhuriyar Nijar.

Ana sa ra san abubuwan da shugaba Keita zai tattauna da takwaransa na kasar Nijar,Mahamadu Isufu ciki har da hulda tsakanin kasashen biyu da maganar da kuma tsaro.

Jamhuriyar Nijar dai na cikin kwamitin samar da zaman lafiya a kasar ta Mali, wanda Algeria ke jagoranta.

Ziyarar ta Mr Keita na zuwa ne bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan mayu daya gabata.

Sai dai yarjejeniyar na fuskantar matsaloli wajen zartar da ita.