"Dole 'yan Nigeria su mallaki katin zama dan kasa"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa a Najeriya, NIMC ta ce dole kowanne dan kasar ya mallaki lambar katin zama dan kasa da ake kira NIN.

Babbar jami'a a hukumar, Hadiza Ali Dagabana, ta shaida wa BBC cewa daga ranar 9 ga watan Janairun 2016 rashin mallakar katin zai haramta wa 'yan kasar abubuwa da yawa ciki har da samun lasisin tuki da katin karbar kudi a banki da sauransu.

Muhimmancin hakan ya sa hukumar ta kara wa'adin yin rajistar samun katin daga karshen watan Satumba 2015 zuwa watan Janairun shekarar 2016.

Jami'ar ta ce hukumar ta yi tanadin wuraren yin rajistar a ko'ina a kasar ciki har da shalkwatar kananan hukumomi.