Kalaman batanci na karuwa a kafofin sadarwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane na amfani da kalaman nuna kiyayya ko na batanci a shafukan sada zumunta na zamani.

Wani bincike da aka gudanar a Najeriya ya nuna cewa ana samun karuwar mutanen da ke amfani da kalaman nuna kiyayya ko na batanci a hanyoyin sadarwa musamman ma shafukan sada zumunta na zamani.

Binciken -- wanda cibiyar McArthur ta gudanar da shi da hadin gwuiwar cibiyar fasahohin zamani ta CITAD, ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Agusta an tattaro kalaman nuna kiyayya ko na batanci fiye da 600 daga shafukan sada zumunta na zamani, wanda kuma ke bukatar a fito da hanyoyin dakile su.

A rahoton da suka gabatar, cibiyoyin biyu sun ce kashi 93 cikin 100 na wadannan kalaman batanci ana yada su ne da harshen turanci , wanda hakan ke nuna cewa yawanci masu yin hakan mutane ne masu ilimi, yayin da aka kuma gano cewa kashi 75 cikin 100 na masu yada wadannan kalamai maza ne.

Shugaban Cibiyar CITAD Malam Yunusa Zakari Ya'u, ya ce za su mika wa hukumomin tsaro irin bayanan da suka tattara domin daukar mataki.

Masana dai sun ce in har hukumomi ba su dauki irin matakin da ya dace ba, to kuwa wannan matsala ta kalaman batanci a kafofin sadarwa na zamani za su lalata zamantakewar al'ummar Najeriya .