Faduwar hannayen jari a Asiya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Farashin hannayen jari ya fadi a Hong Kong da Seoul.

Kasuwar hannayen jari a yankin Asiya ta sake faduwa sakamakon ci gaba da fargabar da ake yi game da bunkasar tattalin arzikin kasar China.

Hannun jari a kasuwar Shanghai ya yi kasa da kashi biyu cikin dari sakamakon faduwar farashin hannayen jari a New York da birnin Landan ranar Talata.

Haka kuma farashin ya fadi a Hong Kong da Seoul, sai dai an dan samu karuwar tashin farashi a Japan.

Wani binciken bangaren 'yan kasuwar China da aka gudanar ya nuna cewa yawan kayayyakin da masana'antun kasar ke fitarwa sun ragu a watan da ya gabata.