An hallaka ma'aikatan Red Cross a Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane a Yemen musamman kananan yara na cikin mawuyacin hali

An harbe har lahira wasu ma'aikatan kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa watau Red Cross a arewacin Yemen.

Kawo yanzu ba'a san wanda ya kashe su ba.

Ma'aikatan biyu-- wadanda dukansu Yamanawa ne na tafiya da wani ayarin motoci daga lardin Saada da ke arewacin kasar zuwa binin Sana'a.

Kungiyar ta Red cross ta kwatanta lamarin a matsayin abin mamaki da ba'a taba ganin irinsa ba.

Red Cross din ta dakatar da dukkan ma'aikatanta daga zirga-zirga a Yemen.

Kisan ma'aikatan ya zo 'yan kwanaki bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari ofishinsu a Aden.