Kyamarar sa ido kan jarirai ba ta da tsaro

Image caption kyamar sa ido kan jarirai

Bincike ya nuna cewa yawancin kyamarori masu farin jini da ake amfani da su wajen sa ido akan jarirai a gida ba su da tsaro.

Za'a iya amfani da kyamarorin wajen sa ido akan jaririrai amma kuma bata gari ka iya amfani da su wajen kai farmaki ga sauran na'urori da ke gidan da kyamarar ta ke.

Ita dai irin wannan kyamarar da kamfanoni daban-daban kerawa ana amfani da ita wajen sa ido kan jarirai a gida, tana aiki ne ta hanyar aika hoton bidiyo zuwa ga shafin intanet na mai ita ko kuma wata manhajar wayar hannu samfurin Android ko komfutar hannu ta tablet.

Rapid 7 kamfanin binciken ya gwada kyamarori guda 7 na kamfanoni daban daban guda 6 a inda ya gano cewa mai kutse zai iya kunna kyamarar ta intanet ya kalli hoton bidiyonta ya kuma yi kutse cikin komfutar da ta ke hade in ji rahoton kamfanin.

Ya kuma gano cewa bayanan da kyamarar ke aikawa ga mai ita ga shafukan intanet ko kuma wayar hannu a bude suke.