Buhari da Osinbajo sun bayyana kadarorinsu

Image caption Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun bayyana kadarorin da suka mallaka

Fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwar da ke bayyana abubuwan da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka mallaka kamar yadda suka gabatar ga hukumar tabbatar da da'a, wato Code of Conduct Bureau.

Sanarwar ta nuna shugaba Buhari ya mallaki kudi kasa da naira miliyan 30 kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, yana kuma da asusun ajiyar banki daya, a Union Bank, amma ba shi da asusun ajiyar banki a kasashen waje, ko wata masana'anta.

Bayanan sun nuna cewa shugaba Buhari ya mallaki gidajen kasa biyu a Daura, daya ya gada daga marigayiya yayarsa dayan kuma daga mahaifinsa.

Yana kuma da gidaje ginin zamani biyu a Kaduna, da daya a Daura da daya a Kano da kuma daya a Abuja.

Sannan yana da filaye biyu daya a Kano daya kuma a Fatakwal wanda kuma har yanzu yana kokarin gano inda yake.

Kazalika, yana da hannayen jari a kamfanonin Berger Paint, da bankin Skye, da kuma bankin Union.

Shugaba Buhari ya mallaki gonaki da shanu 270, da awaki 25, da dawakai biyar.

Shi kuwa mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya mallaki abubuwan da suka hada da gida a unguwar Victoria Garden City da ke Lagos, da kuma wani gidan a unguwar Ikoyi a Lagos.

Yana da gida a kan hanyar Lagos zuwa Ibadan mai daki biyu, sannan yana kuma da gida mai daki biyu a garin Bedford da ke Ingila.

Osinbajo ya kuma mallaki kudi kusan naira miliyan 94.

A baya dai an sha korafi dangane da jinkirin bayyana abubuwan da shugabannin suka mallaka.