Ana tuhumar sojin Faransa da lalata yara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana zargin sojojin Faransa da lalata yara a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Wani babban jami'an kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana tuhumar wani sojan Faransa da yaudarar wata yarinya inda ya yi lalata da ita a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

A yayin da ya kai ziyara kasar, Zeid Ra'ad Al Hussein ya ce yarinyar ta haihu a watan Afrilu ta kuma kai kara domin kotu ta tabbatar da uban dan.

Tuni dai Faransa ta kaddamar da bincike a kan lamarin.

A baya an sha zargin dakarun Faransa da cin zarafin yara a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta inda suke yaudarar su da basu ruwa da abinci su yi lalata da su.

A watan da ya gabata a ka kori shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar saboda irin wadannan zarge-zarge da ake yi wa ma'aikatansu.