Liberia ta kawar da cutar Ebola

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani mutum da ya warke bayan ya kamu da cutar ebola

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana Liberia a matsayin kasar da ta kawar da cutar ebola baki daya a karo na biyu.

A watan Mayun da ya gabata ne ta ce kasar ta kawar da kwayar cutar ta ebola baki daya , sai dai daga bisani an samu wani da ya kamu da cutar a watan Yuni.

Hukumar lafiyar ta ce za a karfafa sa ido a kan ko za a sake samun wani da ya kamu da cutar a cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Kasashen Guinea da Saliyo da ke makobtaka da Liberia kawo yanzu na samun mutanen da ke kamuwa da cutar ta ebola.