'Afrika ta Kudu ta fi yawan attajirai'

Image caption Birnin Johannesburg

Afrika ta Kudu ita ce kasar da ta fi yawan attajirai a Afrika da suka amsa sunan miloniya na dalar Amurka kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

A cewar rahoton da bankin AfrAsia and New World Wealth ya fitar, birnin Johannesburg, da ake yi wa lakabi da birnin zinari shi kadai yana da irin wadannan attajirai watau miloniya-miloniya su 23,400 inda kasar gaba daya ta ke da kashi 30 cikin dari na jumullar attajiran a Afrika.

Birnin Alkahira na kasar Masar shi ne na biyu a yawan irin wadannan attajirai da ke Afrika ya yin da birnin Legas na Najeriya wanda ke matsayi na uku yake da attajiran 9,100.

Rahoton ya bayyana miloniya a matsayin mutumin da ke da dukiyar da ta kai ta akalla dala miliyan daya.

A birnin Accra na kasar Ghana rahoton ya ce ana samun karuwar irin wadannan attajirai duk da cewa, a yanzu yana da mutane 2,300 da dukiyarsu ta kai ta dala mliyan dayan ne kawai duk da baya cikin jerin birane biyar na farko.

Bayan birnin Legas, sai kuma Cape Town harwayau a kasar Afrika ta Kudun wanda ya na da hamshakan attajiran 8,900 yayin da birnin Nairobi na kasar Kenya ya ke da 6,200.