Manyan kasashe Larabawa na kin 'yan gudun hijira?

Image caption Wasu 'yan gudun hijirar Syria da dama da su ke samun mafaka a sansanin MDD a Jordan

A yayin da 'yan gudun hijirar Syria ke kara shiga halin ni-'ya-su a kokarinsu na samun mafaka a Turai, tambayoyi na ta cika zukatan mutane cewa, "Me ya sa ba sa neman shiga manyan kasashen Larabawa masu arziki, wadanda kuma suka fi kusa da Syrian?"

Duk da cewa cikin shekaru da dama da suka gabata, da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Syrian sun samu damar shiga kasashen Larabawa irin su Labanon da Jordan da Turkiya, a bayyane take cewa ba sa tunkurar kasashen Larabawa masu arziki domin neman mafaka.

A hukumance, mutanen Syria na da damar da za su nemi izinin shiga kasashen Larabawa masu arziki domin yawon bude ido ko kuma neman aiki.

Ana rade-radin cewa kasashen Larabawa masu arziki sun sanya tsauraran matakai da za su iya zama kalubale ga mutanen Syria wajen samun izinin shiga.

'Yan kadan din da suka yi nasarar samun izinin shiga wadannan kasashe kuwa, sune wadanda dama tuni suke zaune a can din sai suka yi sa'a aka tsawaita lokacin zamansu, ko kuma wadanda suke da 'yan uwa a can.

"Me ya sa ba a maraba da su?"

'Yan kasar Syria ba za su iya shiga kowacce kasar Larabawa ba ba tare da takardar izinin shiga ba wato biza, sai dai kasashe irin su Algeria da Mauritaniya da Sudan da kuma Yemen.

Ganin irin yadda wadannan kasashe na Larabawa suka fi kusa da Syria suka kuma fi ta arziki ya sa kafofin watsa labarai da na shafukan intanet suka diga ayar tambaya kan cewa "Shin wa ya fi cancanta ya taimakawa 'yan gudun hijirar Syria tsakanin Turai da wadannan kasashen?"

A makon da ya gabata ne aka kaddamar da wani kamfe a shafin twitter wanda aka kirkiro masa maudu'i mai taken "#Welcoming_Syria's_refugees_is_a_Gulf_duty," da ke nufin "hakkin kasashen Larabawa masu arziki ne su bai wa 'yan gudun hijirar Syria mafaka," an kuma yi amfani da wannan maudu'i sau 33,000.

Mutane sun yi ta saka hotuna masu sosa zuciya domin bayyana irin halin da 'yan gudun hijirar Syria suke ciki, kamar hoton da ke nuna mutane sun nutse a ruwa, da wanda ke nuna yadda ake tsallakar da yara ta shingen waya mai tsini mai lantarki da kuma yadda suke bacci a wuri mai datti.

Wani shafin Facebook mai suna "Syrian Community in Denmark," wato "Al'ummar Syria a Denmark" ya rarraba wani bidiyo da ke nuna 'yan gudun hijira lokacin da ake barinsu suke shiga Austria daga kasar Hungary, inda har wani mai shiga shafin ya yi tsokaci cewa: "Ya ya zamu gudo daga nahiyarmu ta 'yan uwa Musulmai wadanda ya dace a ce su suka karbemu fiye da kasar da suke kira ta kafurai ce?"

Image caption Jaridar Saudi Daily Makkah ta wallafa zanen barkwanci a kan kin karbar 'yan gudun hijira da kasar ke yi

"Ku karbi bakuncin su"

Labarin ya ja hankalin kafafen yada labarai na yankin sosai. Wata jarida ta kasar Saudiyya mai suna Saudi Daily Makkah Newspaper, ta wallafa wani zanen barkwanci a shafinta da ke nuna wani Balarabe ya leko ta wata kofa da aka zagaye da shingen waya mai tsini mai lantarki,yana nuna wata kofar da ke kusa da shi mai dauke da zanen tutar Tarayyar Turai.

Duk da irin kiraye-kirayen da ake yi wa kasashen Larabawa masu arziki da su tallafawa 'yan gudun hijirar Syria, babu wata alama da ke nuna cewa sun shirya yin hakan, duk da cewa kuwa kasashen irin su Kuwait da Saudiyya da Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, sun dogara ne da 'yan ci-rani wajen yin ayyukan karfi a kasashen nasu.

Image caption Kasashen Larabawa masu arziki sun dogara da 'yan ci rani wajen yin aikin karfi